logo

HAUSA

Ecowas ta ce yunkurin ficewa da wasu kasashe ke yi daga kungiyar zai haifar da matsala a ayyukan tsaron hadin gwiwa na kungiyar

2024-07-03 09:23:10 CMG Hausa

 

An bude zaman farko na  majalissa ta 6 na kungiyar Ecowas na 2024 a birnin Abuja dake tarayyar Najeriya, inda mahalarta taron suka nuna bukatar mayar da hankali wajen tabbatar da samun kyakkyawar alaka tsakanin cibiyoyin kungiyar da mambobin kasashe.

Yayin taron da aka fara ranar Litinin 1 ga wata, sabuwar shugabar majalissar Mrs Memounatou Ibrahim ta jaddada muhimmancin aiwatar da kudurorin da aka zartar a taron kungiyar da aka gudanar a watan Mayu a jihar Kano.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

 

Ta ce, fara tattaunawa da kuma aiwatar da kudurorin za su taimaka wajen warware dimbin matsalolin da shiyyar ke fuskanta kama daga na siyasa, tattalin arziki da kuma na rashin tsaro da karuwar ayyukan ta’addanci.

Saura kamar yadda ta fada sun hada da na karancin abinci, matsalolin zurga-zurga tsakanin mambobin kasashe da kuma kalubalen sauyin yanayi.

Ta tabbatar da aniyar majalissar na yin aikin tare da cibiyoyin kungiyar Eowas wajen aiwatar da rahoton shugaban hukumar Ecowas a kan ayyukan raya kasa, tare kuma da duba batun samar da kotun musamman da za ta hukunta laifufukan cin zarafin bil Adama da sauran manyan laifufuka da aka aikata a kasar Gambia a tsakanin 22 ga watan Yulin 1994 zuwa 21 ga watan Janairun 2017.

A jawabinsa shugaban hukumar gudanarwa ta kungiyar ta Ecowas Omar Alieu Touray ya ce, babu shakka akwai matsalar babba ta fuskar ayyukan tsaron hadin gwiwa a shiyya da zarar kasashen nan uku sun fice daga cikin kungiyr ta Ecowas, a inda ya ja hankalin kasashen uku cewa muddin dai ba su sauya shawara ba to kuwa ’yan kasar za su iya fuskantar matsaloli kamar haka.

“Ba za su taba samun goyon bayan shiyyar ba a duk lokacin da dan asalin kasashen ke neman wani matsayi a kungiyar tarayyar Afrika ko Majalissar Dinkin Duniya da ma sauran hukumomin kasa da kasa.” (Garba Abdullahi Bagwai)