logo

HAUSA

Abubuwan Ban Al’ajabi Na Ci Gaba Dake Jihar Mangoliya Ta Gida

2024-07-03 08:40:31 CMG Hausa

Jihar Mongoliya ta gida mai cin gashin kanta a arewacin kasar Sin, tana da kan iyaka mai tsawo daga kudu, kuma daga gabas zuwa yamma tana iyaka da Heilongjiang, Jilin, Liaoning, da sauran yankuna dake wurin. A arewa kuma tana iyaka da Mongoliya da Rasha. Mongoliya ta gida tana da kasa mai fadin kilomita miliyan 1.18, wadda ta mamaye kusan kashi 12 cikin dari na daukacin fadin kasar Sin. Tana kuma da yawan jama'a kusan miliyan 25 ko fiye, Hohhot ne babban birnin jihar. Mongoliya ta gida ta taka rawar gani a tarihin duniya fiye da na yawancin kasashe, balle lardunan wata kasa ko daula. Wannan yanki yana da hamadar Gobi mai fadin gaske da kuma filaye mara iyaka. 

Birnin Hohhot, na jihar Mongolia ta gida ya shahara a matsayin “Cibiyar sarrafa madara”. Yankin kyautata lafiya na zamani na Yili tsarin masana’anta ne da ya hade sassan samar da ci gaba mai kunshe da raya sana’ar shuka, da samar da madara, da amfani da na’urorin zamani wajen sarrafa hajojin ta, da kirkire-kirkiren kimiyya da fasahohi, da raya sana’ar yawon shakatawa ta al’adu da samar da nishadi, da gudanar da hada hadar kasuwanci. 

Babban aikin samar da lantarki na Mongolia ta gida muhimmin aikin kasa ne na samar da makamashi. Aikin na kunshe da tsarin zamani da ya hade wasu fasahohi na kirkire-kirkire daban daban wuri guda. Yayin samar da lantarki ta wannan salo ana rage barnata kwal, da ruwa, da lantarki zuwa matsayi mafi kyau a gida da ma kasa da kasa bai daya. Wannan tsari ya tabbatar da salon samar da makamashi abun dogaro kuma mai tsaro, da samar da dumi, da tururi a yankin, ta yadda aka kai ga raya guraben ayyukan yi, da ingiza harkokin tattalin arziki da zamantakewar yankin gaba, kana hakan ya ba da damar cimma nasarar yakin da ake yi da gurbacewar iska.

A halin yanzu, kamfanin samar da hidimar aikewa da sakwanni na ZTO ya bunkasa zuwa kamfani mai hada hadar kasuwanci mafi girma a fannin sa, kana mafi masun ci gaba cikin daidaito a jihar Mongolia ta gida mai cin gashin kai. Cibiyar sa ta tsara rarraba kaya na da na’urori irin su na farko a duk kasar Sin mai amfani da fasahohin zamani na ware kayayyaki, wadanda ke iya aikin da ya kai kaso 90% ba tare da sanya hannun mutum ba, wanda hakan ya sanya ta zama cibiya mai matsayin koli a fasahar rarraba kayayyaki mai amfani da nau’urori masu sarrafa kan su, kana mai na’urori dake iya ware kayayyaki mafi inganci a jihar Mongolia ta gida mai cin gashin kai ta kasar Sin. (Sanusi Chen, Saminu Alhassan, Mohammed Yahaya)