logo

HAUSA

IPO ta duniya: A cikin shekaru goma Sin ke kan gaba a duniya wajen neman izinin lambar kira ta AI

2024-07-03 20:34:00 CMG Hausa

A ranar 3 ga Yuli agogon wurin, hukumar kula da mallakar fasaha ta duniya ko IPO ta fitar da wani rahoto kan yanayin ikon mallakar fasahar samar da bayanai ta amfani da kirkirarriyar basira ko Generative Artificial Intelligence a Turance. Rahoton ya nuna cewa, daga shekarar 2014 zuwa ta 2023, masu fasahar kirkira na kasar Sin sun nemi mafi yawan adadi na lambar kirar mallakar fasahar samar da bayanai ta AI.

Fasahar samar da bayanai ta AI tana ba masu amfani da ita damar kirkirar abubuwa kamar rubutu, hotuna, kida, da lambar kwamfuta, wadanda ke tallafawa jerin masana'antun kira da kuma samar da kayayyakin ga masu bukata. Tsakanin shekarar 2014 zuwa 2023, kasar Sin tana da ikon mallakar fasaha sama da 38000 da ke da alada da fasahar samar da bayanai ta AI, wanda ya ninka ta Amurka da take matsayi na biyu sau shida. (Yahaya)