logo

HAUSA

Sin ta bukaci Isra’ila ta sauke nauyin dake wuyan ta dangane da samar da agajin jin kai a Gaza

2024-07-03 12:01:40 CMG Hausa

Wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Fu Cong, ya yi tsokaci game da matsanancin halin jin kai da jama’a ke ciki a zirin Gaza, lamarin da ya ce ya ta’azzara ne sakamakon matsananciyar kamfar muhimman kayayyakin bukata na yau da kullum, da kalubalen kiwon lafiya.

Fu Cong, ya bayyana hakan ne yayin zaman kwamitin tsaron majalissar da aka gudanar dangane da halin da ake ciki a sassan gabas ta tsakiya, ciki har da batun falasdinu.

Jami’in ya kuma soki lamirin matakin rufe mashigar Rafah sakamakon matakan soji da dakarun Isra’ila ke dauka, wanda hakan ya sanya ala tilas dubban motocin dakon kayayyakin tallafin jin kai dake kan hanyar shiga Gaza dakatawa a mashigar. Kaza lika, ya kuma soki yadda ake ta kai hare hare kan wuraren ajiya da kayan aikin hukumomin samar da agaji dake aiki a wurin, yana mai cewa, sama da ma’aikatan jin kai 200 suka rasa rayukan su a rikicin na Gaza, al’amarin da ya kasance mai matukar tayar da hankali, da ba a taba ganin irinsa ba a tarihi.

Daga nan sai jami’in ya yi kira ga Isra’ila, da ta tabbatar da samar da damar gaggauta shigar da kayayyakin agajin jin kai Gaza, ta kuma ba da cikakken hadin gwiwa ga MDD, da sauran hukumomin ba da agajin jin kai.  (Saminu Alhassan)