logo

HAUSA

MDD ta amince da kudurin da kasar Sin ta gabatar kan hadin gwiwar AI

2024-07-02 13:36:13 CMG Hausa

A jiya Litinin ne babban taron Majalisar Dinkin Duniya (MDD) karo na 78 ya amince da wani kuduri wanda kasar Sin ta gabatar, kuma kasashe sama da 140 suka dauki nauyi, kan karfafa hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa wajen inganta amfani da fasahar kwaikwayon tunanin dan Adam wato AI.

Kudurin kan “habaka hadin gwiwar kasa da kasa kan inganta amfani da fasahar kwaikwayon tunanin dan Adam” ya jaddada cewa, ya kamata bunkasuwar AI ya bi tsarin ka’idojin dan Adam, da inganta fasahohi masu fa’ida da amfani ga Adam.

Kudurin ya karfafa hadin gwiwar kasa da kasa da daukar matakai a zahiri don taimakawa kasashe, musamman kasashe masu tasowa, habaka fasahar AI, da kyautata wakilci da muryarsu yayin da ake gudanar da harkokin AI a duniya, ba da shawara ga "yanayin kasuwanci bisa gaskiya, da adalci, da kuma rashin nuna bambanci," da kuma tallafawa MDD wajen taka muhimmiyar rawa a hadin gwiwar kasa da kasa.

Zaunannen wakilin kasar Sin a MDD, Fu Cong, ya bayyana a yayin gabatar da daftarin kudurin a zauren taron, cewar kudurin da kasar Sin ta gabatar ya mai da hankali ne kan inganta amfani da fasahar AI, tare da ba da shawarar daukar matakai masu muhimmanci da amfani don karfafa hadin gwiwar kasa da kasa.

"Manufar kasar Sin ita ce a taimaka wa dukkan kasashe, musamman kasashe masu tasowa, su amfana daidai da ci gaban AI, da dinke rarrabuwar kawuna, da kyautata tsarin tafiyar da harkokin AI a duniya, da gaggauta aiwatar da ajandar ci gaba mai dorewa ta shekarar 2030," a cewar wakilin. (Yahaya)