Sin ta gabatar da jawabi kan ingiza hakkin mata a gun taron kwamitin kare hakkin bil Adam
2024-07-02 14:06:06 CMG Hausa
Wakilin dindindin na kasar Sin dake Geneva, fadar MDD da sauran kungiyoyin kasa da kasa dake Switerland Chen Xu a madadin kasashe fiye da 80, ya yi jawabi kan yadda za a ingiza aikin kare hakkin mata bisa fasahar kwaikwayon tunanin dan Adam wato AI, a gun taro karo na 56 na kwamitin kare hakkin bil Adam na MDD.
A cikin jawabinsa, Chen Xu ya ce, fasahar AI na ci gaba da samun bunkasuwa cikin sauri a halin yanzu a duniya, wadda ke gaggauta ci gaban tattalin arziki da al’umma da kuma al’adun bil Adam. Mata muhimmin bangare ne na raya al’adun kayayyaki da na tunani, wanda ke taka muhimmiyar rawar gani wajen ingiza bunkasuwar al’umma. Badi za a cika shekaru 30 da zartas da sanarwar Beijing da tsarin aiwatar da harkokinta, dole ne mu yi amfani da wannan dama mai kyau don samun daidaito tsakanin mata da maza, kuma a baiwa mata damar taka rawa wajen raya sabon karfin samar da hajoji da hidimomi masu karko tare da cin gajiyarsa. (Amina Xu)