logo

HAUSA

CMG ya gudanar da baje kolin "Tattaunawa kan wayewar kai" a hedkwatar MDD

2024-07-02 20:06:33 CMG Hausa

 

An gudanar da bikin kaddamar da baje koli na musamman mai taken "Tattaunawa kan wayewar kai" na MDD, wanda babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG ya shirya, a hedkwatar MDD dake birnin New York.

A gun bikin na jiya Litinin, shugaban CMG Shen Haixiong, ya gabatar da jawabi, inda ya ce an zartas da kudurin kafa ranar kasa da kasa ta tattaunawa kan wayewar kai da kasar Sin ta gabatar a babban taron MDD karo na 78, tare da yanke shawarar mayar da ranar 10 ga watan Yunin ko wace shekara a matsayin ranar tattaunawa kan wayewar kai ta kasa da kasa, wanda hakan ya nuna ajandar wayewar kan duniya da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar ta samu matukar karbuwa daga kasashen duniya. (Safiyah Ma)