Mataimakin shugaban tarayyar Najeriya ya ziyarci garin Gwoza domin jajantawa mutanen da harin bom ya shafa
2024-07-02 10:57:39 CMG Hausa
Mataimakin shugaban tarayyar Najeriya Sanata Kashim Shettima ya bayyana damuwarsa kan harin bom din da ya faru a garin Gwoza wanda ya zuwa jiya Litinin mutane 32 ne aka tabbatar da rasuwarsu.
Sanata Kashim Shettima ya ziyarci yankin ne jiya Litinin 1 ga wata, inda shaidawa iyalan wadanda bala’in ya shafa cewa gwamnati ba za ta bari jininsu ya tafi a banza ba, wajibi ne a hukunta masu hannu a wannan hari.
Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.
Mataimakin shugaban na tarayyar Najeriya wanda ya kai ziyara babban asibitin birnin Maiduguri inda ake lura da mutanen da suka samu raunika a yayin harin, ya ce tun lokacin da shugaban kasa ya samu rahoton wannan al’amari hankalinsa yake a tashe, inda ya sha alwashin kara daukar matakai da za su tabbatar da Najeriya ta kasance kasa mai cike da zaman lafiya.
“Zuciyar shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu tana tare da mutanen da wannan harin na bom ya shafa. Wannan ta sanya ya ba mu umarni na musamamn domin mu zo mu gabatar da ta’aziyyarmu da kuma jaje ga wadanda wannan harin bom ya shafa, kuma muna tare ne da darakta janaral na hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa da kuma mukaddashin gwamnan jihar Borno wanda za su yi aiki tare domin duba hanyoyin da za a tallafawa mutanen.”
Mataimakin shugaba na tarayyar Najeriya ya kuma tabbatar da aniyar gwamnatin tarayya na bayar da agaji ga mutanen da harin ya shafa. (Garba Abdullahi Bagwai)