Shugaban Najeriya ya yi alawadai da harin kunar bakin wake a Gwoza dake jihar Borno
2024-07-01 09:26:03 CMG Hausa
Shugaban tarayyar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya yi alawadai da mummunan harin kunar bakin wake da aka kai garin Gwazo dake da tazarar kilomita 135 kudu maso gabashin Maiduguri wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 18 sannan kuma da dama suka samu raunika.
Cikin wata sanarwa dauke da sa hannun mai magana da yawun shugaban Mr Ajuri Ngelale, shugaba Tinubu ya ce, gwamnati ba za ta taba lamunta da irin wannan ta’addanci ba, kuma wajibi a kamo tare da hukunta masu hannu a wannan aika-aika.
Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.
Shugaban na tarayyar Najeriya wanda ya mika sakon jaje da ta’aziyyarsa ga gwamnati da al’ummar jihar Borno bisa faruwar wannan al’amari. Ya tabbatar da cewa, wannan hari ba zai taba sanyayawa dakarun tsaron kasar gwiwa ba wajen tsananta kai hari kan maboyar ’yan ta’adda a duk inda suke.
Ya ce, rayukan ’yan Najeriya suna da matukar daraja a wurin gwamnati kuma za ta yi duk mai yiwuwa wajen kare duk wani dan kasa dake kaunar zaman lafiya da ci gaban kasa a dukkannin matakai.
Daga karshe shugaban na tarayyar Najeriya ya yi kira ga daukacin ’yan kasar da su hada karfi da jami’an tsaro domin dakile ayyukan ’yan ta’adda a kasar baki daya.
A wani labarin kuma, kungiyar gwamnonin arewacin Najeriya ta bayyana alhininta bisa wannan hari na gari na Gwoza.
Shugaban kungiyar gwamnonin, kuma gwamnan jihar Gombe Alhaji Inuwa Yahaya ya bayyana harin a matsayin tsantsar rashin imani wanda duniya baki daya ta yi alawadai.
Ya jajantawa daukacin al’ummar jihar Borno musamman ma iyalai da ’yan uwan wadanda suka rasa rayukansu ko kuma suka samu raunuka a yayin wannan harin. (Garba Abdullahi Bagwai)