logo

HAUSA

An yi bikin nune-nunen shirye-shirye masu inganci da CMG ya tsara a Tajikistan

2024-07-01 11:27:35 CMG Hausa

 

Babban rukunin gidajen talibijin da rediyo na kasar Sin wato CMG da kamfanin dillancin labarai na “Khovar” da gidan talibiji na “Sinamo” sun yi hadin gwiwar gabatar da bikin nune-nunen shirye-shirye masu inganci a Dushanbe, fadar mulkin kasar Tajikistan, a ran 30 ga watan da ya gabata, gabanin ziyarar aikin da shugaban kasar Sin Xi Jinping zai kai kasar, inda zai halarci taro karo na 24 na majalisar shugabannin mambobin kungiyar hadin kai ta Shanghai wato SCO. A cikin bikin nune-nunen, an gabatar da shirye-shirye fiye da 10 ciki har da “Haduwa da Xi Jinping” a wasu muhimman kafofin yada labarai a kasar, ta yadda za a daukaka huldar kasashen biyu da ciyar da hadin kansu gaba bisa labaran da aka gabatar a cikin shirye-shiryen.

A cikin jawabinsa ta kafar bidiyo, shugaban CMG Shen Haixiong ya ce, shirye-shiryen da za a gabatar musamman “Haduwa da Xi Jinping” da “Kiran Hanyar Siliki” ba ma kawai sun mai da hankali kan bunkasuwar kasashen biyu ba, har ma da dukkanin duniya baki daya, kuma ya bayyana ci gaban da aka samu karkashin wasu shawarwari, ciki har da shawarar “ziri daya da hanya daya”. Ya yi imanin cewa shirye-shiryen za su samu karbuwar al’ummar kasar, wadanda ke bayyana cewa, Bil Adam na iya more farin ciki da ci gaba da ma al’adu tare. CMG na fatan zurfafa hadin gwiwa da takwarorinsa a kasar don kara hadin kai da tuntubar juna, da ma zurfafa mu’ammalar ala’du ta yadda za su taka rawar gani wajen ingiza kafa kyakkyawar makomar kasashen biyu ta bai daya a fannin sada daddaden zumunci da amincewa da juna da cin moriya da magance kalubaloli tare. (Amina Xu)