Fadar shugaban Falasdinawa ya ki amincewa da mika Gaza ga sojojin kasa da kasa
2024-07-01 11:02:23 CMG Hausa
A jiya Lahadi ne fadar shugaban Falasdinawa ta yi watsi da duk wani matakin mika yankunan Falasdinu ga wani daga waje, a matsayin martani ga kalaman da Isra'ila ta yi na mika zirin Gaza ga sojojin kasa da kasa.
A cikin wata sanarwa da kamfanin dillancin labarai na WAFA ya fitar, Nabil Abu Rudeineh, kakakin fadar shugaban, ya ce "babu halaccin kasancewar wasu kasashen waje a yankunan Falasdinawa, kuma al'ummar Falasdinu ne kawai za su iya yanke hukunci kan wanda zai tafiyar da harkokinsu da kuma gudanar da al’amurransu."
Ya nanata cewa gwamnatin Isra'ila ta yi batar basira har tana tunanin za ta iya yanke hukunci kan makomar al'ummar Falasdinu tare da tabbatar da mamayar ta hanyar shigo da dakarun kasashen waje.
Ya kuma jaddada cewa, batun Falasdinu batu ne na kasa da ‘yanci, ba wai taimakon jin kai kadai ba, babban al’amari ne kuma mai muhimmanci ga Larabawa. (Yahaya)