Shugaban Mauritaniya Ghazouani ya sake lashe zabe kamar yadda sakamakon wucin gadi ya nuna
2024-07-01 10:22:36 CMG Hausa
Shugaban kasar Mauritaniya Mohamed Ould Ghazouani ya lashe zaben shugaban kasar, a cewar sakamakon wucin gadi na kaso 99.27% na rumfunan zabe da hukumar zaben kasar ta fitar a jiya Lahadi.
An sake zabar Ghazouani ne a zaben da aka gudanar ranar Asabar da sama da kashi 56 cikin dari na kuri’un da aka kada, kamar yadda sakamakon kuri’u daga rumfunan zabe 4,468 cikin 4,503 da aka bayyana a shafin intanet na hukumar zabe mai zaman kanta ta Mauritaniya ya nuna. (Yahaya)