Xi ya aike da sakon taya murna ga sabuwar gwamna-janar na Australiya Samantha Mostyn
2024-07-01 14:22:33 CMG Hausa
A ranar 1 ga watan Yuli, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da sako ga Samantha Mostyn tare da taya ta murna kan kama aiki a matsayin gwamna-janar na Australiya.
Xi ya bayyana cewa, Sin da Australiya muhimman abokan hadin gwiwar juna ne, da muhimman kasashe a yankin Asiya da tekun Pasifik, da kuma muhimman karfi dake tabbatar da daidaito tsakanin kasashen duniya. Kyakkyawan ci gaban dangantakar dake tsakanin Sin da Australiya, ya kasance tushen muhimman muradun kasashen biyu da al'ummomin kasashen biyu, kuma ya dace da zaman lafiya da kwanciyar hankali da bunkasuwa da wadata a shiyyar da duniya baki daya. Ya ce yana mai da hankali sosai kan bunkasuwar dangantakar dake tsakanin Sin da Australiya, kuma a shirye yake don yin aiki tare da bangaren Australiya, wajen gina kyakkyawar dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare tsakanin Sin da Australiya, bisa ka'idojin mutunta juna, da samun moriyar juna, da neman cimma matsaya daya duk da kasancewar bambance-bambance, ta yadda za a samar da karin alfanu ga al'ummomin biyu. (Yahaya)