Ministan wajen Najeriya: Hadin gwiwar Sin da Afirka ya samarwa Afirka damammakin ci gaba
2024-06-30 15:33:21 CMG Hausa
Ministan ma’aikatar harkokin wajen tarayyar Najeriya Yusuf Maitama Tuggar, ya ce karkashin manufofin kasar Sin da suka hada da dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka na FOCAC, da shawarar ziri daya da hanya daya, Sin ta samarwa kasashen Afirka ciki har da Najeriya, wasu damammakin samar da ci gaba na musamman.
Tuggar, wanda ya bayyana hakan yayin zantawa da ‘yan jaridar kafar CMG a kwanan baya, lokacin da yake ziyarar aiki a kasar Sin, ya ce Najeriya na aiki tukuru wajen ingiza hadin gwiwa da Sin a fannoni daban daban, wadanda suka hada da raya layukan dogo, da hanyoyin mota, da bututan iskar gas da lantarki. Ya ce Sin ta zuba jari mai tarin yawa a fannin gina ababen more rayuwa, wanda hakan ya ingiza damar samar da guraben ayyukan yi ga ‘yan Najeriya, kuma hakan ya yi matukar amfanar kasar.
Ministan ya kara da cewa, nahiyar Afirka na bukatar karin jari mai tarin yawa, domin bunkasa fitar da hajojin da aka sarrafa a cikin nahiyar, ba wai kawai kayan da ake fitarwa domin a sarrafa a waje ba. Kuma kasar Sin ta tabbatar da kudurin ta na taimakwa wajen warware wadannan matsaloli, ta kuma nuna matukar goyon bayan ta ga Afirka, ta hanyar juba jari mai yawa a nahiyar.
Ya ce bisa yadda kamfanonin Sin ke shiga ana damawa da su, sashen sarrafa batiran lithium na Najeriya na kara fadada. Kaza lika hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu a fannin sabbin makamashi, zai fadada cin gajiya daga sassan daban daban masu nasaba, ciki har da na kirar ababen hawa masu aiki da lantarki. Kuma baya ga kasuwar cikin gida ta Najeriya, fannin zai kuma samar da hajojin fitarwa zuwa sauran kasashen duniya. Hadin gwiwar sassan biyu zai samar da muhimmin tallafi ga Najeriya a fannin raya masana’antun ta.
Game da batun fasahar kirkirarriyar basira ko AI kuwa, ministan ya ce Najeriya na da matasa masu hazaka, da za su taka muhimmiyar rawa wajen gudanar da hadin gwiwa da Sin a fannin na AI. Don haka ya yi fatan cewa, kasashen biyu za su fadada hadin gwiwa a fannonin musayar al’adu, da ilimi, da harkokin zamantakewa, da horaswa a fannin samar kwarewa. Mista Tuggar ya kara da cewa, Sin ba ta kallon duniya ta fuskar taswirar yankuna, maimakon haka, tana fatan dunkulewa karkashin shawarar ziri daya da hanya daya, ta yadda kasashe da yankunan duniya za su kara kusantar juna. (Saminu Alhassan)