logo

HAUSA

Shirye-shiryen CGTN sun samu lambobin yabo a bikin rediyo da telabijin na kasashen Larabawa

2024-06-30 15:02:06 CMG Hausa

A jiya Asabar, yayin bikin rediyo da telabijin na kasashen Larabawa karo na 24, wanda ya gudana a kasar Tunisia, wasu shirye-shirye guda 2 da sashen Larabci na kamfanin CGTN na kasar Sin ya tsara, sun samu lambobin karramawa masu matsayin farko.

Daya daga cikin shirye-shiryen 2, shi ne shirin telabijin mai taken "A lokacin da Pharaoh, wato sarkin Masar na tsohon zamani, ya ga Sanxingdui na kasar Sin", wanda ya samu lambar yabo a fannin fim game da labarin gaskiya. Ta wannan shiri, an yi bayani kan tarihin Masar, gami da na kasar Sin, da yadda al'adun kasashen 2 ke cudanya da koyi da juna, don nuna darajar tsoffin al'adun gargajiya a zamanin da muke ciki.

Dayan shirin da ya samu lambar yabon kuwa shirin rediyo ne mai taken "Kuruciya a kauyuka", wanda ya shafi labarin yadda wasu matasan kasar Sin suka koma kauyukansu, inda suka kaddamar da wasu sana'o'i, tare da samar da nasu gudunmowa ga kokarin raya kauyuka.

Bikin rediyo da telabijin na kasashen Larabawa, wani kasaitaccen biki ne mai matsayin koli, wanda hadaddiyar kungiyar rediyo ta kasashen Larabawa ta kan shirya sau daya a duk shekara. Tun daga shekarar 2015, aka fara yarda tashoshin telabijin na Larabci na sauran kasashe, wadanda ba na Larabawa ba su halarci gasar shirye-shiryen da ake gudanarwa a wajen bikin. (Bello Wang)