logo

HAUSA

Kasar Sin ta amince da dokar ba da agajin gaggawa da aka yi wa kwaskwarima

2024-06-29 16:20:59 CMG Hausa

‘Yan majalisar dokokin kasar Sin sun amince da dokar ba da agajin gaggawa da aka yi wa kwaskwarima, domin inganta rigakafi, da daukar matakan da suka dace, da kuma kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

Dokar da aka yi wa kwaskwarima, wadda aka zartar a wani zama na zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama’ar kasar Sin ko NPC, za ta fara aiki ne daga ranar 1 ga Nuwamban shekarar 2024.

Dokar da ke kunshe da babi takwas, ta tanadi matakan rigakafi da shirye-shiryen gaggawa, da sa ido da ba da gargadi da wuri, da martanin gaggawa da ceto, da ayyukan farfadowa da sake ginawa, da dai sauransu. (Yahaya)