logo

HAUSA

Tattalin arzikin Najeriya ya samu karuwar Naira biliyan 309 ta bangaren aikin gona a shekarar bara kadai

2024-06-29 17:28:21 CMG Hausa

Ministan harkokin noma da bunkasa samar da abinci na tarayyar Najeriya Sanata Abubakar Kyari ya ce tattalin arzikin kasar ya samun gagarumin karuwa na tsabar kudi har Naira biliyan 309 a sakamakon amfanin gonar da aka samu a 2023.

Ministan ya tabbatar da hakan ne ranar Alhamis 27 ga wata lokacin da yake zantawa da manema labarai jim kadan da kammala taron majalissar tattalin arziki na kasa karkashin jagorancin shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Sanata Abubakar Kyari ya ce an samu wadannan kudade ne a fannin noman alkama kadai wanda aka samu noma tan dubu dari hudu da saba’in da hudu da dari shida da ashirin da takwas, kuma an samu nasarar hakan ne bayan da gwamnati ta tallafawa manoma alkama har dubu dari da bakwai da dari hudu da ashirin da tara da kayan aikin noma.

Ministan gonar ya ci gaba da cewa, domin dakile hauhawar farashin kayan abinci, gwamnatin tarayyar ta rabar da sama da tan dubu sittin na ingantaccen irin shuka ga manoman kasar, baya ga magungunan kwari da kayayyakin aikin gona da aka baiwa manoma daban daban domin dai bunkasa sha’anin noman abinci a kasa.

Har ila yau ministan ya sanar da cewa, a yanzu haka ma’aikatar tasa ta karbi buhuna miliyan biyu da dubu goma sha biyar na takin zamani daga baban bankin kasar CBN domin rabawa ga manoma.

“A saboda haka muna kira ga gwamnatocin jahohi da su gaggauta zuwa domin dibar kason da aka ware musu domin rabawa ga manoman jihohinsu kasancewar damuna ta kankama”.

“Kuma za a raba takin ne kyauta”.(Garba Abdullahi Bagwai)