logo

HAUSA

A ko da yaushe Sin ta kasance mai gina zaman lafiya a duniya, mai ba da gudummawa ga ci gaban duniya, kuma mai kare tsarin kasa da kasa

2024-06-29 21:26:49 CMG Hausa

 

Masu kallonmu, bana ce ta cika shekaru 70 da kafa ka'idoji 5 na zaman tare cikin lumana. Yau shekaru 70 da suka gabata, firaministan kasar Sin Zhou Enlai ya gabatar da wadannan ka'idoji 5 gaba daya a karon farko, wadanda suka hada da mutunta ikon mallakar kasa da cukakkun yankunan kasa, rashin cin zarafi tsakanin juna, rashin tsoma baki cikin harkokin cikin gidan juna, samun daidaito da moriyar juna, da yin zaman tare cikin jituwa. A cikin shekaru 70 da suka gabata, kasashen duniya sun amince da wadannan ka'idojin 5, wadanda kuma suka zama muhimman ka'idoji wajen tafiyar da dangantakar kasa da kasa da kuma muhimman ka'idojin dokokin kasa da kasa.