Sin ta sauke nauyin dake bisa wuya wajen raya hulda tsakanin kasa da kasa
2024-06-29 16:40:22 CMG Hausa
Yau shekaru 70 da suka gabata, an nemi ‘yancin kan kasashen Asiya da Afirka da Latin Amurka, sabbin kasashe suna son tabbatar da ikon mallakarsu da raya tattalin arzikinsu. Shugabannin kasar Sin sun gabatar da ka’idoji 5 na zaman tare cikin lumana tsakanin kasa da kasa a karo na farko, batun da ya samar da hanyar raya hulda tsakanin kasa da kasa.
A halin yanzu, ana tinkarar babban sauyi a duniya. Yayin da ake fuskantar kalubale wato wace irin duniya za a raya? Ta yaya za a raya duniya? Kasar Sin ta gabatar da manufar raya al’umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil Adama.
Daga ka’idojin 5 zuwa manufar raya al’umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil Adama, kasar Sin ta kyautata sauke nauyin dake bisa wuyanta wajen raya hulda tsakanin kasa da kasa, da tabbatar da zaman lafiya da samun ci gaba, da kuma kiyaye odar kasa da kasa cikin adalci.
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da muhimmin jawabi a taron murnar cika shekaru 70 na ka’idoji 5 na zaman tare cikin lumana tsakanin kasa da kasa, inda ya jaddada cewa, ya kamata a bi ka’idojin kiyaye ikon mallakar kasa da samun adalci da girmama juna, da yin kokarin samun zaman lafiya da tsaro, da yin hadin gwiwa wajen samun wadata tare, da bin tunanin kiyaye adalci, da kuma ci gaba da bude kofa ga kasashen waje. Wannan ya shaida cewa, ana aiwatar da ayyuka bisa ka’idojin 5, kuma an bude sabon babi a wannan fanni.
Yanzu, kasar Sin tana kokarin raya kasa mai karfi da farfado da al’ummar Sinawa ta hanyar zamanintarwa irin ta kasar Sin, kana tana fatan kasa da kasa za su yi hadin gwiwa tare da ita don samun bunkasuwa tare. (Zainab Zhang)