Kamfen saida shimkafa a farashi mai rahusa domin fuskantar hauhawar farashin abinci a kasuwa a Nijar
2024-06-29 17:16:16 CMG Hausa
Mu tafi a jamhuriyyar Nijar inda ministan kasuwanci da masana’antu Seydou Asman ya kaddamar da kamfen da zai shafi tsawon wata guda domin saida shimkafa a farashi mai rahusa tun daga ranar 26 ga watan Junin shekarar 2024 har zuwa sauran yankunan kasar domin rage kaifin tsadar rayuwa ga al’umma.
Daga birnin Yamai, abokin aikinmu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto.
Bisa bukatar shugaban kwamitin ceton kasa na CNSP, birgadiye janar Abdourahamane Tiani, ma’aikatar kula da cimaka ta kasa OPVN ta kaddamar da wannan gagarumin aikin saida shimkafa a farashi mai rahusa bisa taken zancen kasa, labou sanny.
Aikin da ta hanyarsa, ma’aikatar OPVN ta tsaida matakin saida buhun shimkafa mai nauyin kilo 25 a kudin sefa jika goma sha uku da rabi. Inda aka kebe kebabbun wurare a birnin Yamai da sauran yankunan kasa, domin taimakawa al’umma samun wannan shimkafa. A cewar hukumomin Nijar, wannan mataki na da burin kawo sauki ga iyalai masu rauni, da kuma kokarin ganin wannan shimkafa ta kai ga mutane cikin sauki.
Ayyukan saida wannan shimkafa na gudanar a karkashin babban darektan OPVN, kanal Sidi Mohamed.
Ministan kasuwanci da masana’antu Seydou Asman ya bayyana cewa, gwamnatin Nijar ta saye wannan cimaka domin al’umma, bisa farashin da aka yi nazari, sefa jika 13500 buhu guda sabanin jika 17000 ko fiye da haka da ake gani a cikin kasuwanni.
A cewar ministan kasuwanci da masana’antu, wannan matakin saida shimkafa a farashi mai rahusa shi ne na tabbatarwa ‘yan Nijar cewa hukumomin kasar Nijar za su ci gaba da cika alkawuran da suka dauka har wata guda na saida wannan shimkafa .
Tun yau da ‘yan watannin baya bayan nan, kayan abinci suka yi tashin gobron zabo a kasuwanni, lamarin da ya fara tada hankalin magidanta masu dan karamin karfi.
Mamane Ada, sashen hausa na CMG daga Yamai a jamhuriyar Nijar.