logo

HAUSA

Kungiyar alkalai ta Jamhuriyar Nijar SAMAN ta janye da yajin aikinta na sa’o’i 72

2024-06-29 16:49:52 CMG Hausa

Wani rikicin aiki tsakanin alkalai da ‘yan sanda kan wasu al’amura biyu da suka faru a jihar Konni da yankin Tillabery da ke jamhuriyar Nijar,  ya tura kungiyar SAMAN shirin shiga yakin aiki na kwanaki uku. Amma daga baya a cikin wata sanarwa a ranar jiya 28 ga watan Yuni, kungiyar SAMAN ta janye yajin aikinta bisa wasu dalilai.

Daga birnin Yamai, abokin aikimu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto.

 

Sanarwar na mai cewa bisa la’akari da taron manema labarai na kungiyar alkalai ta kasa SAMAN a ranar 24 ga watan Yunin shekarar 2024.

Bisa la’akari da takardar yajin aiki na kwanaki uku, ranar 1, 2 da 3 ga watan Yulin shekarar 2024, da kungiyar ta ajiye a ma’aikatar shari’a da ‘yancin dan Adam a ranar 26 ga watan Yunin shekarar 2024.

Haka kuma, bisa la’akari da  tashin hankali da ya abku a kauyen Tassia na jihar Tera da ya yi sanadiyar mutuwar sojojin Nijar 21 da kuma zaman makokin da gwamnatin Nijar ta ayyana na kwanaki uku game da wannan tashin hankali.

Bisa wadannan dalilai ne, kungiyar alkalai ta kasa SAMAN ta dauki niyyar janye yajin aikinta na sa’o’i 72 a dukkan fadin kasa a ranar jiya Juma’a 28 ga watan Yunin shekarar 2024 domin nuna juyayinta ga al’ummar Nijar da ke cikin zaman makoki.

Sai dai duk da haka, kungiyar alkalan Nijar ta bayyana cewa, tana bisa bakanta na maido da yajin aikinta, idan har dai ba’a magance matsalolin da suka kai ta ga daukar niyyar tsunduma yajin aiki ba.

A karshen sanarwar ta bakin Doubou Yahaya, babban sakatare janar din kungiyar ya bayyana, da dukkan sunan al’akalan Nijar baki daya ya fatan kwanciyar hankali da zaman lafiya a cikin kasa, da neman gafarar ubangiji Allah ga dukkan sojojin da suka kwanta dama wajen kokarin kare kasar Nijar daga hare haren ta’addanci.

Mamane Ada, sashen hausa na CMG daga Yamai a jamhuriyyar Nijar.