logo

HAUSA

Asusun IMF ya rage hasashen saurin karuwar GDPn Amurka

2024-06-28 10:37:59 CMG Hausa

Asusun lamuni na duniya IMF, ya rage hasashen saurin karuwar GDPn Amurka na shekarar 2024 daga kashi 2.7 cikin dari da aka yi a watan Afrilu zuwa kashi 2.6 cikin dari. A sa’i daya kuma, asusun wanda ya fitar da sabon hasashen a jiya Alhamis, ya yi imani cewa, hadarin bashin Amurka da ma manufofin cinikayyarta ba kawo cikas kadai za su yi ga ci gaban tattalin arzikinta ba, har ma da haifar da hadari ga tattalin arzikin kasa da kasa.

IMF ta bayyana cewa, gibin kasafin kudin na Amurka yana da girma, bashin da ta ci ma yana ta karuwa. Inda ta yi gargadin cewa, manufofin cinikayya masu muni da Amurka take aiwatarwa ma na iya kawo hadari. (Safiyah Ma)