Wang Yi ya yi jawabi a liyafar murnar cika shekaru 70 da fitar da ka’idoji 5 na zaman tare cikin lumana
2024-06-28 20:49:05 CMG Hausa
Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya yi jawabi a gun liyafar murnar cika shekaru 70 da fitar da ka’idoji 5 na zaman tare cikin lumana tsakanin kasa da kasa wanda aka gudanar a yau, inda ya yi nuni da cewa, tun daga fitar da ka’idojin 5 na zaman tare cikin lumana tsakanin kasa da kasa, zuwa raya al’umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil Adama, an shaida cewa, Sin na kokarin neman hanyoyin raya hulda tsakanin kasa da kasa, kana ta kiyaye sauke nauyin dake bisa wuya, wajen tabbatar da zaman lafiya da samun ci gaba a duniya, da kuma kiyaye odar kasa da kasa cikin adalci.
Wang Yi ya jaddada cewa, aikin bin ka’idojin 5 ba zai kare ba, kana ana kokarin raya al’umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil Adama. Kasar Sin tana son yin kokari tare da sauran sassan kasa da kasa, wajen fadada hadin gwiwa, da yin mu’amala da juna, don tinkarar kalubale, da raya duniya mai kyakkyawar makoma tare. Don haka, kasar Sin ta ba da shawarar cewa, ya kamata a girmama juna, da raya hadin gwiwa da sada zumunta da juna, da more tsarin kiyaye tsaro, da sa kaimi ga samun bunkasuwa da wadata ta hanyar bude kofa da hadin gwiwa, da raya al’adun bil Adawa, ta hanyar amincewa bambance-bambance, da koyi fasahohi da juna, ta yadda za a gina kyakkyawar makomar raya duniya mai adalci. (Zainab Zhang)