logo

HAUSA

EU da Ukraine sun rattaba hannu kan yarjejeniyar tsaro

2024-06-28 10:24:09 CMG Hausa

Tarayyar Turai (EU) da kasar Ukraine, sun rattaba hannu kan wata yarjejeniyar tsaro, yayin wani taron majalisar gudanarwar EU da aka yi a birnin Brussels.

Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya halarci taron, inda ya sanya hannu kan yarjejeniyar tare da shugaban majalisar Charles Michel da shugabar hukumar EU Ursula von der Leyen, yayin wani biki.

Daftarin yarjejeniyar ya yi tanadin cewa, EU ta kuduri niyyar ci gaba da samarwa Ukraine da al’ummarta dukkan tallafin da suke bukata ta fuskar siyasa da kudi da tattalin arziki da jin kai da soji da diplomasiyya ba tare da kayadadden lokaci ba, matukar ta na bukata.

EU ta kuma amince ta yi amfani da kudin shigar da ake samu daga kadarorin Rasha da aka kakabawa takunkumai, wajen tallafawa Ukraine. (Fa’iza Mustpha)