logo

HAUSA

CGTN ya nuna yadda mutanen Asiya ke kallon Amurka

2024-06-28 15:11:48 CMG Hausa

Wani binciken jin ra'ayin jama'a ya gano cewa, hargitsi na cikin gida da tsangwama da rikici, da kuma mulkin kama karya sun kasance siffar Amurka a ko da yaushe.

Kafar yada labarai ta CGTN ta babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin (CMG) da jami'ar Renmin ta kasar Sin ne suka gudanar da binciken, ta hannun cibiyar sadarwa ta kasa da kasa ta sabon zamani. An gudanar da binciken ne tsakanin wasu mutane daga kasashen Asiya.  

A cikin binciken, kashi 84.4 cikin dari na masu amsa sun yi imanin cewa, tashin hankali sanadiyyar harbe-harben bindiga, ya zama cuta mai tsanani a cikin al'ummar Amurka, kuma kashi 75.4 cikin dari na masu amsa sun yi imanin cewa, akwai wariyar launin fata mai tsanani a Amurka.

Bugu da kari, binciken ya gano cewa, kashi 69.1 cikin dari na masu amsa tambayoyi daga Asiya, sun zargi Amurka da daukar ma’aunoni biyu ga dokokin kasa da kasa. Kashi 64.4 cikin 100 kuma sun yi imanin cewa takunkuman da Amurka ta sanyawa wasu kasashe, wani mataki ne na haifar da matsi kan tattalin arzikinsu tare da yi musu mulkin mallaka. Kashi 67.4 cikin 100 na masu amsa kuma, sun soki Amurka saboda kakkaba wasu ka'idoji da ra'ayoyinta a kan sauran kasashe, da kuma yin watsi da dokokin da kasashen duniya suka amince da su. Har ila yau, kashi 67.9 cikin dari na masu amsa sun yi imanin cewa, Amurka tana amfani da girman dala don tura  matsalolin tattalin arzikinta na cikin gida ga al'ummomin duniya, kana  kashi 74.4 cikin dari na masu amsa sun yi imanin cewa Amurka kasa ce mai mulkin kama karya.

An gudanar da binciken ne tsakanin mutane 2009 daga kasashen Asiya guda 10, da suka hada da Singapore da Saudiya da Thailand da Hadaddiyar Daular Larabawa da Philippines da India da Indonesia da Malaysia da Pakistan da kuma Japan. (Safiyah Ma)