Hukumomin agaji na MDD sun kara yawan agajin da suke kai wa Darfur da Khartoum na Sudan
2024-06-27 13:21:55 CMG Hausa
Hukumomin agaji na MDD sun ce sun hada hannu da abokan huldarsu, domin bunkasa yawan agajin da ake kai wa wurare masu fama da rikici a Darfur da Khartoum, musammam El Fasher, babban birnin jihar North Darfur.
A cewar asusun kula da kananan yara na MDD (UNICEF), sama da yara 400 ne aka bayar da rahoton an kashe ko sun jikkata yayin rikicin na baya-bayan nan. Yana mai cewa, ci gaba da amfani da ababen fashewa a yankunan jama’a na kara barazana ga fararen hula da ma’aikatan agaji.
Shi kuwa shirin samar da abinci na duniya WFP, ya bayar da rahoton cewa, yana raba muhimman kayayyakin abinci da na gina jiki ga sama da mutane 135,000 a jihar Al-Jazirah dake yankin gabas maso tsakiyar kasar. Wannan ne kuma karo na farko da kayayyakin WFP ke isa yankin na Sudan mafi samar da amfanin gona, tun bayan fadadar rikicin zuwa Wad Madani, babban birnin jihar a watan Disamba.
Shirin na WFP ya kuma bayar da rahoton cewa, jerin gwanon motoci dauke da sama da ton 2,300 na tallafin abinci ga maza da mata da yara 164,000, ya tsallake kasar Chadi inda ya nufi arewaci da tsakiyar Darfur. (Fa’iza Mustapha)