logo

HAUSA

Sin na fatan tattaunawa tare da EU game da shirin bincike kan motocin EVs don cimma kyakkyawar matsaya

2024-06-27 19:51:10 CMG Hausa

Ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin, ta ce ana fatan shawarwarin da za a gudanar tsakanin bangarorin Sin da kungiyar Tarayyar Turai ta EU, game da aniyar EUn ta gudanar da bincike kan batun samar da rangwame a fannin kirar motocin Sin masu amfani da lantarki ko EVs, za su kai ga cimma kyakkyawan sakamako.

Da yake tsokaci kan hakan, yayin taron manema labarai na Alhamis din nan, kakakin ma’aikatar He Yadong, ya ce, "Ana fatan EU da Sin za su hadu a tsakiya, su cimma nasarar warware takaddama idan da ali, kana su cimma nasarar amincewa da matsaya guda, ta yadda za a kai ga kaucewa kara ta’azzarar turka-turkar cinikayya, wadda ka iya shafar alakar tattalin arziki da cinikayyar sassan biyu."

He Yadong ya kara da cewa, hadin gwiwar Sin da EU na kunshe da ribar moriyar juna, kuma sassan biyu na da babbar dama ta gudanar da hadin gwiwa, a fannin sauya alkibla zuwa samun ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba." (Saminu Alhassan)