logo

HAUSA

Gwamnatin tarayyar Najeriya tare da ASUU sun cimma yarjejeniya wadda ta dakile yunkurin tafiya yajin aiki

2024-06-27 09:43:31 CMG Hausa

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta cimma yarjejeniya da kungiyar malaman jami’o’in kasar ASUU a kan wasu batutuwan da suka shafi malaman.

Yayin zaman sulhu da bangarori biyun suka gudanar jiya Laraba 26 ga wata a birnin Abuja, an cimma yarjejeniyar cewa za a ci gaba da tattaunawa domin warware matsalolin malamai cikin ruwan sanyi ba tare da tafiya yajin aiki ba.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi bagwai ya aiko mana da rahoto.

Ministan ilimi na tarayya Farfessa Tahir Mamman ne ya jagoranci taron da shugabannin kungiyar malaman jami’o’i a harabar ma’aikatar ilimi dake birnin Abuja. Farfesa Tahir Mamman ya tabbatar da cewa, tun daga jiya Laraba gwamnati ta fara tuntubar masu ruwa da tsaki domin ganin an hanzarta shawo kan matsalolin dake damun ilimi a kasar baki daya.

“Akwai tuntuba da za mu ci gaba da yi a kan wasu bayanan da ba mu da su kuma muna bukatarsu, haka kuma za mu hada kai da wasu ma’aikatu da suke da ruwa da tsaki domin warware matsalolin.”

A jawabinsa shugaban kungiyar malaman jami’o’in ta kasa Farfesa Emmanuel Osodeke ya ce, yana fatan gwamnati za ta bi dukkannin batutuwan da aka zartar yayin taron.

A kan batun wa’adin da kungiyar ta diba kuwa na tafiya yajin aiki nan da makwanni biyu, shugaba kungiyar ASUU ya ce, za su yi zama da mambobin kungiyar domin sanar da su batutuwan da aka zartar yayin taron nasu na jiya da bangaren gwamnatin tarayya. (Garba Abdullahi Bagwai)