logo

HAUSA

Wang Lili: Tana Kiyaye Neman Cimma Nasara A Kan Wasan Kwallon Kwando

2024-06-27 21:18:20 CMG Hausa

Kafin horaswar kungiyar wasan kwallon kwando ta mata mai mutane 3 ta kasar Sin a yammacin ranar farkon watan Yuni, Wang Lili wadda ta zo filin wasa a karon farko bayan tsawon watanni fiye da 8 rabuwarta da filin wasa ta ce, kafin horaswar, ta tuna ta kiyaye kafar hagu mai dauke rauni a cikin mafarkinta. A cikin zuciyarta, tana jin tsoron sake samun rauni a kafar, don haka tana gani kafar a cikin mafarkinta.

A birnin Chengdu, Wang Lili ta karbi kofin lambar yabo ta ‘yar wasa mafi hazaka wato MVP ta wasan kwallon kwando na mata mai mutane 3 na kakar da ta gabata da hukumar hadin gwiwar wasan kwallon kwando ta duniya wato FIBA ta gudanar. Amma ba ta koma filin wasa ba. Lokacin da take zauna a gefen filin wasan, ana iya ganin alamar rauni a kafarta ta hagu. A watan Satumba na shekarar bara, ta kara samun rauni a kafarta karo na biyu.

A yayin wasan karshe na gasar shekara-shekara ta wasan kwallon kwando na mata mai mutane 3 na hukumar FIBA na kakar shekarar 2023, wato wasan dake tsakanin kungiyar Sin da ta Faransa, Wang Lili ta ji rauni domin ta fadi kasa a wasan. A sakamakon hakan, jijiyar da ta hada kashi biyu wadda ta gurde a shekarar 2016 ta sake samun rauni. A lokacin, akwai saura watanni 10 kawai kafin a bude gasar wasannin Olympics ta birnin Paris.

Wang Lili ta bayyana cewa, tun daga lokacin da ta sake jin rauni a kafarta, ta fara yin kidayar lokacin da ta samu sauki da koma filin wasa. Ta ce, wasu lokuta tana ganin watakila ba za ta shiga filin wasan gasar wasannin Olympics a karo na biyu ba.

Wang Lili ta ce, lokacin warkewa daga rashin lafiya bai yi daidai da sauran ‘yan wasa ba, domin ta samu rauni kan wuri daya sau biyu, kuma an sake yin aikin tiyata a kafar. Likita ya ce, akwai bambanci a kafar bisa na tiyatar da aka yi a karo na farko, kana shekarunta ya yi yawa, ba kamar na matasa ba, akwai wuya yiwuwar samun farfadowa cikin sauri.

Wang Lili mai shekaru 31 da haihuwa ita ce ‘yar wasa mafi yawan shekaru a cikin kungiyar wasan kwallon kwando na mata mai mutane 3 ta kasar Sin a halin yanzu. Ta fito ne daga kungiyar wasan kwallon kwandon mata ta jami’ar Peking, ta buga wasa a gasar wasan kwallon kwandon mata ta kasar Sin wato WCBA a kakar shekarar 2014 zuwa 2015. Bayan hakan, ta taba shiga kungiyar wasan kwallon kwandon mata ta kasar Sin sau da yawa, amma ba ta zama ‘yar wasa mafi muhimmanci a cikin kungiyar ba. Har zuwa gasar wasannin Olympics ta birnin Tokyo da aka gudanar a shekarar 2021, ita da abokan wasa na kungiyar wasan kwallon kwando na mata mai mutana 3 ta kasar Sin sun samu lambar tagulla. Wang Lili tana sanya rigar wasa mai lamba 23, kuma tana da kwarewa sosai a buga wasa, don haka masu sha’awar wasan suna kiran ta da suna “Jordan mace ta kasar Sin”.

Bayan hakan, kungiyar ta ci gaba da samun lambobin yabo masu yawa. A shekarar 2022, kungiyar ta samu lambar yabo ta tagulla a gasar cin kofin duniya, kuma ta zama zakara a gasar cin kofin Asiya, Wang Lili ta zama ‘yar wasa mafi hazaka wato MVP a wasan. A kasar Sin, Wang Lili ta taba samu maki 60 a cikin wasa daya, don haka ta zama ‘yar wasa ta biyu da ta samu maki 60 a cikin wasa daya a gasar WCBA. A shekarar 2023, Wang Lili ta samu lambobin yabo na MVP sau da dama, dukkan ‘yan wasan da kungiyoyin wasan suna maida hankali ga wannan ‘yar wasa mai lamba 23 ta kasar Sin.

Amma bayan gasar cin kofin duniya ta shekarar 2023, kungiyarta da ita sun tinkari kalubale. Kungiyarta tana da burin zama matsayi na uku na gaba, amma ba ta cimma hakan ba. A lokacin, Wang Lili ta ji rashin dadi sosai, amma a matsayin ‘yar wasa, ta samu farfadowa bayan wasu kwanaki. Amma ta samu babban rauni. Da farko dai, Wang Lili ta kasa fahimtar wannan yanayi, a kullm tana tambayar kanta.

Koda yake irin wannan rauni ba zai kawo karshen rayuwar ‘yar wasa ba, amma ana bukatar dogon lokaci na samun sauki, hakika za a kawo sauyi ga shirin yin horaswa, har ma ga makomar ‘yar wasan. A sa’i daya kuma, abokan wasan kungiyarta da ‘yan wasan sauran kungiyoyin wasa, suna kiyaye yin kokarin samun ci gaba, gasa ba ta tsaya domin ta ba, wasanni ba za su jira kowa ba.

Wang Lili ta bayyana cewa, bayan da aka yi mata aikin tiyata, ta fuskanci mawuyacin hali, domin ba ta iya tsalle ko gudu ba, har ma ba ta iya yin tafiya cikin sauri ba. Ta ce, idan ba ta karfafa wa kanta gwiwa ba, yana  yiwuwa ba za ta iya daidaita yanayin ba.

A lokacin kuruciyarta, Wang Lili ta taba samun matsala da mahaifinta a dalilin buga wasan kwallon kwando, amma ta ce a rayuwarta ta yau da kullum, ita ba mai yawan magana ba ce, idan aka ambato wasan kwallon kwando, sai dai halinta ya canja sosai.

Tun daga lokacin da take buga wasan kwallon kwando tare da yara maza a garinta, wannan mace ta kasance mai muhimmanci a filin wasa, ta kan yi gudu sosai, da yin tsalle sosai, kana ba ta jin tsoron buga wasa a fili. Wang Lili ta ce, wannan ne halinta a filin wasan kwallon kwando.

Wang Lili ta kara da cewa, wani mai horaswa nata ya taba gaya mata cewa, ya kamata a nemi samun nasara a kan wasa, sai dai wasu lokuta akan cimma nasara ko a ci tura. A ganin Wang Lili, a matsayin wata ‘yar wasa, ya kamata a yi hamayya da sauran ‘yan wasa, da yin kokarin cimma nasara.

A wannan karo, a yayin tinkarar raunin da take ji, Wang Lili tana kokarin cimma nasarar daidaita shi. Wang Lili ta kara yin kuzari wajen samun sauki da neman komawa filin wasa cikin sauri. Koda yake akwai sauran watanni 10 kawai suka rage kafin gasar wasannin Olympics ta Paris, amma a sakamakon kokarin da take yi, tawagarta ta yi bincike da cewa, akwai yiwuwar dawowarta filin wasa cikin lokaci. A yayin da ta samu irin raunin lokacin shekarunta kai 24 da haihuwa, ta kashe watanni shida da samun lafiya da komawa filin wasa. Amma yayin da shekarunta suka kai 31 da haihuwa a halin yanzu, ya kamata ta kara yin kokari, amma ba ta saduda ba.

A yammacin ranar farkon watan Yunin, kafin ta sake koma filin wasa bayan tiyatar da aka yi mata, Wang Lili ta ambato mafarkin da ta yi ga abokan wasanta, kana ta gaya musu cewa, domin ba ta shiga filin wasa da buga wasa tare da sauran ‘yan wasa har na tsawon watanni 8 ba, idan ta gamu da matsala ko ba ta buga wasan da kyau ba, ya kamata su gaya mata a filin.

Lokacin da ta buga wasa a filin wasa, Wang Lili tana ganin ta iya buga wasan kamar lokacin da. Ta bayyana cewa, koda yake tana damuwa kafin buga wasan, amma idan ta shiga filin wasan, babu komai a cikin kwakwalwarta sai wasa kawai, tana cike da hankali kan buga wasan.

Wang Lili ta ce, idan tana buga wasa a fili, ta kan ji muryoyin abokan wasanta suna cewa, suna bayanta babu damuwa, ta ce, wannan ya karfafa ta, abokan wasanta suna tare da ita.

Ya zuwa yanzu, kungiyar wasan kwallon kwando na mata mai mutane 3 ta kasar Sin ta riga ta samu izinin halartar gasar wasannin Olympics ta birnin Paris da za a gudanar a shekarar bana, za a gabatar da sunayen membobin kungiyar. Wang Lili ta ce, ta taba kai ziyara a birnin Paris lokacin da ta buga gasar wasan a Turai, tana begen samun damar sake zuwa birnin don halartar gasar wasannin Olympics a birnin. (Zainab Zhang)