logo

HAUSA

Sin na shirin harba sabbin na’urorin binciken samaniya don zurfafa nazari

2024-06-27 20:18:31 CMG Hausa

Kasar Sin ta shirya harba sabbin na’urorin binciken samaniya da suka hada da Tianwen-2 zuwa shekarar 2025, domin binciken baraguzai dake shawagi a sararin samaniya, kana za ta harba na’urar Tianwen-3 wajen shekara ta 2030, don kwaso samfura daga duniyar Mars, da kuma na’urar Tianwen-4 wurin shekara ta 2030 don binciken tsarin duniyar Jupiter.

Da yake tsokaci kan hakan a Alhamis din nan, yayin taron manema labarai, mataimakin shugaban hukumar kula da harkokin binciken sararin samaniya ta kasar Sin ko CNSA Bian Zhigang, ya ce a nan gaba, ayyukan Sin game da binciken samaniya za su kara karkata ne ga nazarin kimiyya, irinsu binciken tushe da sauye-sauyen tsarin gudanar duniyoyin dake kewaye da rana, da tasirin kananan taurari, da tasirin rana kan duniyar bil Adama, da ma sauran halittun dake wajen doron duniya.

Bian ya ce, Sin za ta yi aiki tare da sauran sassa, wajen gina cibiyar binciken duniyar wata ta kasa da kasa, tare da raba nasarorin binciken kimiyya da fasaha da aka samu tare da abokan tafiya.   (Saminu Alhassan)