logo

HAUSA

MDD ta yi kira da a kara magance matsalar miyagun kwayoyi

2024-06-27 11:19:48 CMG Hausa

 

Babban sakataren MDD António Guterres ya yi kira ga kasashen duniya da su kara daukar matakan kandagarki don magance matsalar amfani da miyagun kwayoyi da sufurinsu tun daga tushe.

Antonio Guterres ya yi kiran ne jiya Laraba, a jawabin da ya gabatar albarkacin ranar yaki da miyagun kwayoyi ta kasa da kasa.

A cewarsa, mutane fiye da dubu 100 na rasuwa sakamakon amfani da miyagun kwayoyi fiye da kima a kowace shekara a duniya, lamarin dake  barazana ga lafiyar jiki da rayuwar jama’a, tare da ba masu aikata laifufuka da ’yan ta’adda kwarin gwiwa.

Kazalika Guterres ya kara da cewa, taken ranar a wannan karo shi ne “Illar a bayyane take: Kara mayar da hankali kan matakan rigakafi”, inda ya bayyana cewa, mataki mafi ma’ana wajen yaki da miyagun kwayoyi shi ne kawar da su daga tushe, wato daukar matakan rigakafi don hana yaduwarsu.

Bisa rahoton da ofis mai bincike laifufuka da miyagun kwayoyi na majalisar ya fitar a wannan rana, yawan mutanen da suka sha miyagun kwayoyi a shekarar 2022 ya kai kimanin miliyan 292, wanda ya karu da kashi 20% bisa na shekarar 2012, wato matsalar ta kara tsananta. (Amina Xu)