logo

HAUSA

Dalian: An rufe dandalin tattaunawa na Davos na lokacin zafi karo na 15

2024-06-27 20:50:50 CMG Hausa

An rufe taron dandalin tattaunawa na Davos na lokacin zafi karo na 15, a yau Alhamis a birnin Dalian dake kasar Sin. Wakilai fiye da 1700 daga kasashe da yankuna fiye da 100 ne suka halarci taron bana, mai taken “Sabon ci gaba a nan gaba”, inda suka tattauna game da fannonin sabon tsarin raya tattalin arzikin duniya, da huldar dake tsakanin Sin da duniya, da tunanin ‘yan kasuwa a lokacin raya fasahar AI, da sabon tsarin ci gaban sana’o’i, da zuba jari kan ci gaban dan Adam, da huldar dake tsakanin yanayi, da halittu, da makamashi da sauransu.

Masu halartar taron sun amince cewa, kasar Sin tana kokarin raya sabon karfin samar da hajoji da hidimomi masu karko, da sa kaimi ga samun bunkasuwa mai inganci, don inganta karfinta na samun bunkasuwa da kanta, da samar da gudummawa ga raya tattalin arzikin duniya, da kuma kara samar da damar hadin gwiwa ga kamfanonin kasa da kasa baki daya.

(Zainab Zhang)