Kungiyar FIFA ta yanke shawarar baiwa Nijar nasasar ci 3 da 0 tsakaninta da Congo
2024-06-27 09:37:44 CMG Hausa
Kungiyar kwallon kafa ta duniya FIFA ta dauki matakin baiwa kasar Nijar nasara. Mataki da ke nufin cewa ’yan wasan kungiyar MENA-Nijar sun doke kasar Congo-Brazaville da ci 3 da 0, a cikin tsarin tankade da rairaye na cin kofin du duniya.
Daga birnin Yamai, abokin aikinmu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto.
Shi dai wannan mataki, ya biyo bayan kin amincewar kasar Congo-Brazaville na zuwa buga wasanta tare da kasar Nijar a birnin Kinshasa, inda kasar Congo ta nace cewa ba za ta buga wasanta ba idan ba ka birnin Brazaville ba ne, bayan lura da cewa filin wasan kwallon kafa na Brazaville bai amsa sharudan karbar wasannin kungiyar kwallon kafa ta Afrika CAF ba.
Alhali kuma ’yan wasan kasar Nijar sun isa domin buga wasansu a birnin Kinshasa amma kuma ’yan wasan kasar Congo-Brazaville suka ki halarta a wasan da ya kamata a buga a ranar 6 ga watan Yunin shekarar 2024.
A cikin wasikar da ta aika ma kungiyar kwallon kafa ta kasar Congo, kungiyar FIFA ta yi amfani da kuduri mai lamba 58 na kundin ladabtarwa na FIFA, da kuma kwamitin ladabtarwa ya shawarta hukunta kungiyar kwallon kafa ta kasar Congo bisa tushen abubuwan da suka biyo baya.
Na farko, wasa tsakanin Congo da Nijar da ya kamata a buga ranar 6 ga watan Junin shekarar 2024 cikin tsarin tankade da rairaye cin kofin duniya FIFA 2026 ya nuna cewa kasar Congo ta rasa wasanta da ci 3 da 0.
Na biyu, an yanke ma kungiyar kwallon kafar kasar Congo hukuncin biyan tara na kudin Suisse CHF dubu 10.
Wannan mataki, masu sha’awar tamaula sun jima suna dakonsa, musammun ma kungiyar kwallon kafa ta kasar Nijar FENIFOOT da ’yan Nijar baki daya ganin cewa wannan mataki ya baiwa kungiyar NEMA wucewa domin wasanninta na gaba. (Mamane Ada)