logo

HAUSA

JKS za ta gudanar da taro kan gyare-gyare a gida daga ranar 15 zuwa 18 ga Yuli

2024-06-27 15:22:40 CMG Hausa

Jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin za ta gudanar da taro na 3 na kwamitin kolinta karo na 20, a ranar 15 ga watan Yuli, a birnin Beijing.

A cewar taron ofishin kula da harkokin siyasa na kwamitin kolin da aka yi yau Alhamis, taro karo na 3 wanda zai nazarci batutuwan da suka shafi kara zurfafa gyare-gyare a gida da inganta zamanantar da kasar Sin, zai gudana har zuwa ranar 18 ga watan Yuli.

Shugaban kasar Sin kuma sakatare janar na kwamitin kolin JKS, Xi Jinping ne ya jagoranci taron na yau. (Fa’iza Mustapha)