logo

HAUSA

Wakilin Sin ya yi kira da a dakatar da bude wuta don kiyaye yara

2024-06-27 14:26:06 CMG Hausa

Wakilin dindindin na kasar Sin dake MDD Fu Cong ya bayyana ra’ayin Sin a wata muhawarar MDD da aka yi a jiya Laraba, kan alakar yara da rikice-rikice, inda ya yi kira ga kasashen duniya da su dakatar da bude wuta don kiyaye yara.

Fu Cong ya kara da cewa, a karshen bara, asusun kula da yara na majalisar ya yi gargadin cewa, zirin Gaza ya zama wuri mafi hadari ga yara a duniya. Ya ce rikicin da ya dabaibaye wannan wuri har tsawon watanni 8 ya kwace rayukan yara Palasdinawa fiye da dubu 15, yana mai cewa dole ne Isra’ila ta saurari kiran da aka yi mata, ta dakatar da kai hari kan daukacin al’ummar Palasdinu.

A cewarsa, abin da ya kamata a sa a gaba shi ne dakatar da bude wuta a zirin Gaza nan da nan da tabbatar da kai tallafin jin kai, da ma gurfanar da wadanda suka aikata laifin cin zarafin yara. Ya ce Sin na kuma kira ga kasashen duniya musamman ma kasashe masu karfi da su taka rawar gani don dakatar da masifar jin kai a wurin. Haka zalika, Sin na goyon bayan rukuni mai kula da matsalar yara da rikice-rikice na kwamitin sulhu da ya nazarci halin da yaran Gaza ke ciki don daukar matakan da suka wajaba. (Amina Xu)