Sin ta zargi Amurka da kitsa karairayi da nufin bata mata suna
2024-06-27 20:44:37 CMG Hausa
Kakakin ma’aikatar tsaron kasar Sin Wu Qian, ya soki lamirin Amurka game da yadda take kitsa karairayi domin bata sunan sauran kasashe, yana mai cewa, Sin ba za ta amince da hakan ba.
Wu Qian, wanda ya bayyana hakan a Alhamis din nan, yayin taron manema labarai, lokacin da aka yi masa tambaya game da rahotannin da wasu kafofin watsa labarai suka fitar, wadanda suka shafi yadda Amurka ke sukar alluran rigakafin COVID-19 da Sin ta samar, da ma yadda Sin din ta raba tallafi ga kasashe masu tasowa dake sassa daban daban na duniya, yayin da ake fama da ibtila’in cutar, ya ce ba wannan ne karon farko da Amurka ke yada karairayi game da Sin ba, kuma ba zai zamo karo na karshe ba.
Ya ce, an sha jin hakan, tun daga batun wai "Sin na haifar da barazanar soji", da batun wai "Ana fuskantar kutse ta yanar gizo daga Sin", Amurka ta sha kitsa karairayi daban daban, da nufin karkatar da tunanin al’umma. To sai dai kuma a cewar jami’in, sassan kasa da kasa na kara fahimtar ainihin halayyar Amurka, ta kitsa karairayi marasa ma’ana.
Daga nan sai Wu ya yi kira ga Amurka da ta yi karatun ta nutsu, ta kare kimarta a matsayin ta na babbar kasa mai karfin fada-a-ji, kana ta dakatar da kirkirar karairayi domin cimma moriyar kashin kai. (Saminu Alhassan)