logo

HAUSA

Kotun Amurka ta sanar da sakin Assange bayan cimma wata yarjejeniya

2024-06-26 13:49:44 CMG Hausa

Julian Assange da ya kirkiro shafin kwarmata bayanai na Wikileaks, ya amsa aikata laifi guda na keta dokar cin amanar kasa a wata babbar kotun tarayya dake Saipan, babban birnin Arewacin Tsibirin Mariana, a matsayin wani bangare na yarjejeniyar da ya cimma da ma’aikatar shari’a ta Amurka, domin kaucewa kara zaman kaso, tare da kawo karshen shari’ar da aka dauki shekaru ana yi.

Duk da ya amince da aikata laifi guda na samu da yada bayanan sirri da suka shafi tsaron kasa ta haramtacciyar hanya, za a kyale Assange ya koma Australia ba tare da zaman kaso a Amurka ba.

Ma’aikatar shari’a ta kasar ta amince ta saurari karar a wani tsibiri a yankin Pasifik, saboda Assange ba ya son zuwa cikin Amurka. (Fa’iza Mustapha)