logo

HAUSA

Wakilin Sin: A magance janyo babban rikici a Gabas ta Tsakiya

2024-06-26 11:04:23 CMG Hausa

Fu Cong, zaunannen wakilin kasar Sin a Majalisar Dinkin Duniya, ya halarci taron tattauna kan batun Falasdinu da Isra'ila na kwamitin sulhu na Majalisar, a ranar Talata. Inda ya ce kasar Sin tana kira ga dukkan bangarori masu ruwa da tsaki da su yi hakuri, su kaucewa daukar matakan da ka iya tsananta halin da ake ciki, da janyo babban rikici mafi tsanani ga daukacin yankin Gabas ta Tsakiya.

Jami'in ya ce, kasar Sin ta yi kira ga wasu kasashen da suke da babban tasiri kan kasashen da batun ya shafa, da su nuna adalci, da rashin karkata ga wani bangare, tare da samar da gudunmawa ta gaske ga yunkurin samun tsagaita bude wuta tsakanin Isra'ila da Falasdinu.

Ban da haka, ya ce kasar Sin ta bukaci kasar Isra'ila da ta dauki hakikanan matakai don kawo karshen cin zarafin Falasdinawa fararen hula, da daina kafa matsugunan Yahudawa, wanda ke girgiza tushen ikon mulki na gwamnatin al'ummar Falasdinawa. (Bello Wang)