Shugaban tarayyar Najeriya ya ce zai tuntubi gwamnonin jihohi kafin yanke shawarar karshe game da sabon tsarin albashi
2024-06-26 09:29:00 CMG Hausa
Shugaban tarayyar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya sanar jiya Talata 25 ga wata cewa, zai tuntubi gwamnonin jihohi da shugabannin kamfanoni masu zaman kansu kafin fitar da alkaluman karshe na sabon tsarin mafi kankantar albashi ga ma’aikatan kasar.
Shugaban ya bayyana hakan ne yayin taron majalissar zartarwa ta kasa da ya gudana a fadar gwamnati dake birnin Abuja. Ya ce, sai bayan ya kammala ganawar ne za a gabatarwa majalissar kasa kudurin dokar sabon tsarin albashin kafin fara aiwatar da dokar.
Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.
A lokacin da yake karin haske ga manema labarai a game da taron majalissar zartarwar, ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na kasa Alhaji Muhammed Idris ya ce, an gabatarwa majalissar kunshin rahoto dake nuna fara amfani da sabon tsarin albashin, to amma kuma sabo da abin ya shafi kasa baki daya ya sanya aka jingine batun gefe guda har sai shugaban ya kammala ganawa da gwamnoni da kuma shugabannin kamfanoni masu zaman kansu.
“Sabon tsarin mafi kankantar albashi na kasa kamar yadda na sha fada ba al’amari ba ne da ya shafi gwamnatin tarayya ba kadai, ya shafi gwamnatocin jihohi, ya shafi kananan hukumomi, sannan kuma ya shafi kamfanoni masu zaman kansu, wannan shi ne ya sanya ake kiransa da sabon tsarin albashi na kasa, a don haka akwai bukatar a fadada tuntuba kafin kaiwa ga matakin turawa majalissar dokoki ta kasa.” (Garba Abdullahi Bagwai)