Ya Kamata A Ba Da Muhimmanci Kan Kimiyya Da Fasaha
2024-06-26 07:26:29 CMG Hausa
Kimiyya da fasaha ke riƙe da mabudin ci gaban kowace ƙasa. Suna taka muhimmiyar rawa wajen samar da arziki, da kyautata rayuwar jama'a, da ci gaban tattalin arziki da sauyi na haƙiƙa a kowace al'umma. Bincike ya nuna cewa akwai alaƙa mai ƙarfi tsakanin habakar ilimin kimiyya da fasaha na ƙasa da yawan kudin shiga na ƙasa a kan kowane mutum. Wannan yana nuna cewa kimiyya da fasaha na da mahimmanci wajen ci gaban tattalin arziki, saboda yana haifar da bincike, da ƙirƙirar sabbin abubuwa wadanda ke haifar da sabbin masana'antu, da ayyukan yi, da ƙimar tattalin arziki. Tun bayan juyin juya halin masana'antu, kasashe masu arziki da ma masu tasowa sun maida hankali kan habaka kimiyya da fasaha kuma suna samun bunƙasuwa sosai.
Daga shekara ta 1870 zuwa yanzu, kasashe masu ci gaba a fannin kimiya da fasaha sun zama masu arziki kuma yawan ci gabansu bai ragu ba. Rashin kula da ilimin kimiyya da fasaha a matsayin matakin samun ci gaba ya haifar da lalacewar da ba za ta iya misaltuwa ba ga wanzuwar kamfanoni. Matsalolin tattalin arzikin da aka gaza shawo kansu, da rashin aikin yi, da durƙushewar harkokin kiwon lafiya da ilimi, da rashin tsaro, da hauhawar farashin kayayyaki, da durƙushewar ababen more rayuwa, a wasu ƙasashe masu duk suna da nasaba da rashin mai da hankali kan kimiyya da fasaha, wanda hakan ke jaddada muhimmanci kimiyya da fasaha ga ci gaban ƙasa.
A cikin jawabinsa a babban taron kimiyya da fasaha na kasar Sin, da babban taron ba da lambar yabo a fagen kimiyya da fasaha na ƙasar, Shugaba Xi Jinping ya jaddada cewa, idan har kimiyya da fasaha za su bunƙasa, to ƙasar za ta bunƙasa, kuma idan kimiyya da fasaha suka yi ƙarfi, ƙasar za ta yi ƙarfi. Zamanintar da kimiyya da fasaha za ta taimaka wajen zamanantar da ƙasar Sin, kuma ingantacciyar ci gaba za ta dogara ne kan ƙirƙirar kimiyya da fasaha don samar da sabbin ƙarfin samar da hajoji da hidimomi. Dole ne mu amince da matsayin jagorancin kimiyya da fasaha bisa manyan tsare-tsare da muhimmiyar rawarsu, da himmantuwa wajen gina ƙasar Sin ta zama ƙasa mai ƙarfi a fannin kimiyya da fasaha nan da shekarar 2035.