logo

HAUSA

Shugaban kasar Nijar Abdourahamane Tiani ya gana da tsoffin shugabannin kasar Bénin Nicephore Soglo da Boni Yayi a Yamai

2024-06-26 09:26:36 CMG Hausa

A jamhuriyyar Nijar, tsoffin shugabannin kasar Bénin Nicephore Soglo da Boni Yayi tun fara ziyarar shiga tsakani. Bayan tarbonsu a ranar 24 ga watan Yuni. Manyan jami'an biyu sun gana tare da shugaban kasar Nijar Abdourahamane Tiani a ranar jiya 25 ga watan Junin shekarar 2024.

Daga Yamai abokin aikinmu Mamane Ada ya aiko mana wannan rahoto. 

Sa'o'i 24 tun bayan shigowarsu a ranar jiya a birnin Yamai, wadannan tsoffin shugabannin kasar Bénin, da suka hada da Dieudonné Nicephore Soglo da kuma Thomas Boni Yayi. Wadannan manyan jami'an biyu sun samu ganawa tare da shugaban kwamitin ceton kasa na CNSP kuma shugaban kasa, Abdourahamane Tiani a fadar shugaban kasa dake birnin Yamai. Wannan ganawa ta gudana a gaban ido faraminista kuma ministan kudi Ali Mahamane Lamine Zeine, da ministan cikin gida birgadiye-janar Mohamed Toumba da kuma darektan fadar shugaban kasa dokta Soumana Boubacar. Tsoffin shugabannin biyu, sun yi musanya musamman kan rikicin dake gudana a yanzu Haka tsakanin Nijar da Bénin.

Haka kuma, wannan ziyara ta wadannan manyan jami'an Benin a kasar Nijar, ta kasance mai matukar muhimmanci gaske ganin yadda al'umomin kasashen biyu suka zura ido suna jiran ganin yadda za'a sulhunta wannan rikici da tuni ya zama mai sarkakiya. 

Abin da mutanen kasashen biyu suke fatan gani shi ne ganin an kawo karshen wannan rikici cikin ruwan sanyi tare da kuma fatan ganin hukumonin kasar Nijar sun gaggauta bude iyakokinsu da Bénin.

Mamane Ada, sashen Hausa na CMG, daga Yamai a jamhuriyyar Nijar.