Ya kamata Sin da Amurka su nuna matukar adawa da sabon salon yakin cacar baka
2024-06-26 20:48:25 CMG Hausa
Mukaddashin jakada a ofishin jakadancin Sin dake kasar Amurka Jing Quan, ya ce kamata ya yi Sin da Amurka su nuna matukar adawa da sabon salon yakin cacar baka, su kuma kaucewa amfani da batun tsaron kasa ta mummunar hanya, tare da siyasantar da batutuwan tattalin arziki da cinikayya.
Da yake tsokaci yayin taron masu ruwa da tsaki na hada-hadar zuba jari na bana, mai lakabin "Select America", wanda babbar cibiyar bunkasa cinikayya ta Sin dake Amurka ta shirya da yammacin ranar Litinin, Jing Quan, ya ce ya kamata Sin da Amurka su martaba juna, musamman martaba manyan jigon moriyar su, irinsu ikon mulkin yankuna da tsarin gudanar da siyasa.
Jami’in ya ce, abu ne mai muhimmanci a samu tattaunawa ba tare da wata tangarda ba, a kuma shawo kan bambance-bambance ta hanyar tattaunawa da shawarwari, musamman domin kaucewa amfani da batun tsaron kasa ta hanyar da ba ta dace ba, da siyasantar da batutuwan tattalin arziki da cinikayya. Wajibi ne a zakulo sabbin hanyoyi na yin nazari, da kofofin shiga tafarkin hadin gwiwar cimma moriyar juna, a fannoni irinsu na tattalin arziki da cinikayya, da noma da raya ilimi, da yawon bude ido, da yaki da cutar daji, da kula da tsoffi da kirkirarriyar basira. (Saminu Alhassan)