logo

HAUSA

Yawon bude ido da baki suka yi a kasar Sin ya samu tagomashi a bana

2024-06-26 10:43:18 CMG Hausa

Kasuwar yawon bude ido da baki daga ketare suka yi a kasar Sin ta ci gaba da farfadowa a bana, inda ake sa ran adadin baki masu yawon bude ido zai kai kaso 80 na matakin da ya kasance a shekarar 2019, kafin annobar COVID-19.

Wannan na kunshe ne cikin wani rahoto kan ci gaban bangaren tsakanin shekarar 2023 da ta 2024, da cibiyar nazari kan harkokin yawon bude ido ta kasar Sin ta fitar jiya Talata.

A cewar rahoton, al’adun kasar Sin da yanayin rayuwa mai inganci su ne abubuwan da suka fi jan hankalin masu yawon bude ido baki da suka zo kasar daga ketare, inda wani nazari da aka yi ya nuna cewa, sama da kaso 60 na masu yawon bude ido baki sun bayyana al’adun kasar Sin a matsayin babban dalilinsu na ziyartar kasar. (Fa’iza Mustapha)