Masana: Aikin dawo da samfura daga bangaren wata mai nisa ya kasance muhimmin ci gaban dan Adam a kimiyya da fasaha
2024-06-26 21:33:32 CMG Hausa
Bangaren na’urar binciken duniyar wata ta Chang’e-6 mai dauke da samfuran duniyar wata mai nisa, ya sauka ba tare da matsala ba a kasar Sin a jiya Talata. Masana na kasashen duniya sun yaba matuka da aikin binciken duniyar wata da na’urar ta Chang’e-6 ta yi a wannan karo. Suna cewa, wannan muhimmin ci gaban ne da aka samu a kimiyya da fasaha a duk fadin duniya.