logo

HAUSA

Nijar na zaman makoki kwanaki 3 bayan mutuwar sojojinta 21 a cikin wani harin kungiyoyin ‘yan ta’adda

2024-06-26 18:46:44 CMG Hausa

Ma’aikatar tsaron kasar Nijar ta zagi a ranar Talata 25 ga watan Junin shekarar 2024 da wani harin kungiyoyin ‘yan ta’adda kan wani sansanin soja da ke yankin Tillabery, tare da kashe sojoji 20, da raunata gomai, da kashi farar hula guda.

Haka kuma ma’aikatar tsaron a cikin sanarwarta ta tabbatar da kashe goman ‘yan ta’adda a yayin wannan hari.

Hukumomin Nijar sun annaya zaman makoki na kwanaki uku a dukkan fadin kasar Nijar.

A ranar Talata, 25 ga watan Junin shekarar 2024, wajen karfe 10 na safe bisa agogon wurin, wani ayarin rundunar jami’an tsaro na FDS ya ci karo da wani harin kungiyoyin ‘yan ta’adda a yammacin kasar, in ji ma’aikatar tsaron kasar Nijar a cikin wata sanarwa da aka karanto ta gidan talabijin na kasa Tele Sahel.

Harin da faru a kewayen kauyen Tassia a shiyyar Tera da ke cikin yankin Tillabery, in ji wannan sanarwa.

Jihar Tera na cikin yankin Tillabery, dake cikin yankin iyaka uku da suka hada kasashen Nijar, Mali da Burkina Faso ya kasance yankin da ‘yan ta’addan kungiyoyin da ke da alaka da IS da Al-Qaida suka samu gindin zama.

Mamane Ada, sashen hausa na CMG daga Yamai a jamhuriyyar Nijar.