logo

HAUSA

Kasar Sin Za Ta Ci Gaba Da Yin Aiki Tare Da Abokan Hulda Don Yin Amfani Da Sararin Samaniya Cikin Lumana

2024-06-25 20:32:06 CMG Hausa

A yau Talata ne bangaren na’urar binciken duniyar wata ta Chang'e-6 da ke dauke da samfurin wata ya sauka a gundumar Siziwang dake jihar Mongoliya ta Gida mai cin gashin kanta ta kasar Sin.

Da take amsa tambayoyi a taron manema labaru da aka saba yi, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta bayyana cewa, kasar Sin a shirye take ta ci gaba da hada kai da abokan huldar kasa da kasa masu ra'ayi iri daya, don yin bincike a sararin samaniya, wanda ya kasance yankin dan Adam na bai daya, da kuma ci gaba da yin kokari wajen yin amfani da sararin samaniya cikin lumana, wanda ya kasance al'amari na bai daya na dan Adam. (Yahaya)