Sin na fatan bangarori daban-daban a Somaliya za su daidaita sabani ta hanyar shawarwari
2024-06-25 11:39:15 CMG Hausa
Mataimakin wakilin dindindin na kasar Sin a Majalisar Dinkin Duniya, Dai Bing, ya gabatar da jawabi yayin da ake nazarin batun kasar Somaliya a kwamitin sulhu na majalisar a jiya Litinin, inda ya yi kira ga bangarori daban-daban na Somaliya, da su yi la’akari da muradun kasa da na jama’a, domin shawo kan sabani ta hanyar shawarwari.
Jami’in ya yi kira ga bangarori daban-daban da su yi kokarin tafiyar da harkokin siyasa cikin lumana. A cewarsa, Sin ta yi maraba da shawarwarin da aka yi tsakanin gwamnatin tarayya ta Somaliya da gwamnatocin jihohin kasar a watan Mayun bana, inda suka tattauna kan wasu muhimman batutuwan da suka shafi duba kundin tsarin mulkin kasar da tsarin shirya zabe. Ya ce ya dace sassan kasa da kasa su bi ka’idar “jama’ar Somaliya su ne jigo, kuma su ne masu kasar”, kuma kada su matsa wa kasar lamba ko su yi shisshigi cikin harkokinta. (Murtala Zhang)