Ministan harkokin wajen Najeriya ya yi tsokaci kan dangantakar kasarsa da kasar Sin
2024-06-25 15:49:47 CMG Hausa
A halin yanzu, ministan harkokin wajen tarayyar Najeriya, Amb. Yusuf Maitama Tuggar, yana wata ziyarar aiki a kasar Sin, inda ya yi shawarwari tare da takwaransa na kasar Sin Wang Yi, da halartar cikakken zama na farko na kwamitocin gwamnatocin Sin da Najeriya a Beijing, da taron shekara-shekara na Davos na lokacin zafi wato Summer Davos karo na 15 a birnin Dalian na kasar.
Kafin tafiyarsa zuwa birnin Dalian don halartar taron Summer Davos, abokiyar aiki, Fa’iza Muhammad Mustapha ta zanta da Amb. Yusuf Maitama Tuggar, inda ya yi tsokaci kan hadin-gwiwar Najeriya da Sin a fannoni daban-daban. (Murtala Zhang)