logo

HAUSA

Xi: A shirya Sin take ta daukaka dangantakarta da Poland zuwa sabon matsayi

2024-06-25 09:36:35 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi alkawarin kasar Sin ta shirya hada hannu da Poland wajen ingiza dangantakar da ke tsakaninsu zuwa sabon matsayi da kara tabbaci da daidaito a duniya mai cike da sarkakiya.

Xi Jinping ya bayyana haka ne jiya Litinin a Beijing, lokacin da yake tattaunawa da takwaransa na Poland Andrzej Duda, wanda ke ziyarar aiki a kasar Sin.

Shi ma firaministan Sin Li Qiang, ya gana da shugaba Andrzej Duda a jiyan, inda ya bayyana kudurin Sin na inganta tsara manufofin samun ci gaba tare da Poland. (Fa’iza Mustapha)