Li Qiang ya gana da shugaban dandalin tattaunawar tattalin arzikin duniya
2024-06-25 20:22:57 CMG Hausa
A safiyar ranar 25 ga wata ne firaministan kasar Sin Li Qiang ya gana da Klaus Schwab, shugaban taron dandalin tattaunawar tattalin arzikin duniya ko WEF a takaice a birnin Dalian da ke arewacin kasar Sin.
Li Qiang ya ce, farfadowar tattalin arzikin duniya a halin yanzu yana da rauni, kuma yana da matukar muhimmanci a lalubo sabbin hanyoyin ingiza bunkasuwa. Kasar Sin ta gabatar da shirin daukar matakin “fasahar kwaikwayon tunanin dan Adam” wato Artificial Intelligence + ne don kara wa bunkasuwar tattalin arziki kuzari ta hanyar fadada yin amfani da fasahar kwaikwayon tunanin dan Adam.
Li Qiang ya bayyana cewa, tafiyar hawainiyar da ci gaban tattalin arzikin duniya ke yi a cikin 'yan shekarun nan, tana da nasaba sosai da yadda kasashe daban daban suka katse mu’amala da wasu ta wasu hanyoyi, da kuma ba da kariya. Kamata ya yi mu kasance da budaddiyar zuciya, da zurfafa hadin gwiwar moriyar juna, tare da yin aiki tare domin nemo sabbin hanyoyin ci gaban tattalin arziki.
A nasa bangare kuwa, Schwab ya ce, a hali mai sarkakkiya da ake ciki a duniya, karfafa hadin gwiwar kasa da kasa na da muhimmanci fiye da yadda aka bukata a da. Taron dandalin tattaunawar tattalin arzikin duniya ya kuduri aniyar ci gaba da yin hadin gwiwa tare da kasar Sin, domin sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arzikin duniya cikin kwanciyar hankali da lumana, da daidaita kalubalen duniya tare. (Yahaya)